Ko ina akwai na Allah: Wani mutumi ya mayar da N1.8m da ya tsinta a cikin kwalin Indomie da ya siya

0
684

Wani dan Najeriya da aka bayyana sunan shi da Mr Chidiebere Ogbonna, ya mayar da naira miliyan daya da dubu dari takwas (N1.8m), wanda ya tsinta a cikin kwalin indomie da ya siya.

A yadda rahoton ya nuna, kwalin Indomie din an saka Indomie din kadan a ciki, inda sauran kuma aka cika da kudi ‘yan naira 1000.

Chidiebere ya ce bayan ya isa gida, ya bude kwalin Indomie din, yana ganin abinda ke ciki yayi gaggawar mayar da kudin zuwa wajen da ya siyo Indomie din.

Da aka tambayeshi dalilin da ya sanya ya dawo da kudin duk da wannan matsalar tattalin arziki da wahala da ‘yan Najeriya suke ciki, sai ya ce kudin ba nashi bane, saboda haka bashi da wani dalili da zai saka ya ajiye cinye kudin.

Mai shagon da ya sayi Indomie din wanda ya cika da farin ciki, yayi masa godiya, sannan yace masa ya dinga zuwa yana karbar Indomie a shagon a duk lokacin da yake bukata, daga wannan lokacin har zuwa watan Disambar wannan shekarar.

To dama dai ance ko ina akwai na Allah, domin kuwa ba duka ne aka taru aka zama daya ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here