Ko a jikina kashe bakar fata da ake yi a kasar Amurka – Cewar Huddah Monroe

0
702

Fitacciyar mai amfani da kafar sadarwa ‘yar kasar Kenya, Huddah Monroe ta ce bata jin dadin nuna wariyar launin fata da ake yiwa bakaken fata a kasar Amurka, sai dai kuma ta ce ba ta yi damuwar da har za ta je ta dinga babatu ba, saboda maza bakar fata basa son mata bakar fata sun fi son zuwa wajen Turawa.

Ta ce maza bakar fata suna tunawa da mata ‘yan uwansu a lokacin da suka shiga wani hali. Ta ce a duk lokacin da suka zama wasu a rayuwa basa neman bakar fata sun fi zuwa su nemi Turawa.

Ta ce bakar fata suna jin kunyar aurar bakar fata ‘yan uwansu, inda suke ganin Turawa sun fi su. Ta kara da cewa duka Baturiyar da ta ke zaune da bakar fata tana zaune da shine saboda kudin shi.

Ta ce har sai komai ya daidaita a bangaren maza bakar fata da mata bakar fata, kafin ta fito ta damu kanta akan kisan da ake yiwa bakar fata a kasashen duniya.

Ta ce: “Wajen da bakar fata ba zai yi rayuwa ba cikin kwanciyar hankali ba wuri bane da zan iya zama. America ba wurin zama bace a wurina, Naje can lokuta da dama, amma ban taba jin kwanciyar hankali ba.”

Source: Linda Ikeji Blog

KU KARANTA: An ceto ‘yammata 69 da aka yi safarar su kasar Turai aka mayar da su bayi

Ta kara da cewa: “Cin zarafin da ‘yan sanda suke yi ba daidai bane, amma yadda maza bakar fata suke wulakanta mata bakar fata shi yafi damunta.

“Ba zan taba zuwa nayi zanga-zanga a kansu ba. Saboda a duk lokacin da suka samu kudi Turawa sun fi bakar fata a wajensu.

“Ya kamata mata bakar fata su farga, kada ku bari wani ya ci zarafin ku ko ya saka ku dauki kan ku ba komai ba, saboda ku ba Turawa bane. Kuna da kyau kun sani dai!

‘Mazajen mu sune suke tilasta mata su canja launin fatarsu, saboda sun fi son Turawa fiye da bakar fata.

“Da yawa daga cikin bakar fata da suka yi sa’ar rayuwa suna nuna wariya ga mutanensu. Bai taba faruwa dani ba, amma na sha ji suna magana a kai. Saboda haka mu gyara halayen mu ta kowanne fanni.

“Wani mahaukaci zai yi tunanin soyayya da auren Baturiya ita ce za ta saka ya zama wani a rayuwa. Daga yaya baza su kashe ka ba?

‘Baturiya na zama da bakar fata ne kawai saboda kudinshi, ba wai saboda yana da kyau ba. Na ga yadda suke yiwa samarinsu ai, amma su kuma kauyawa suna tunanin sun zama wasu ne a rayuwa.

‘A lokacin da abubuwa suka canja masa a lokacin ne zai fara tunanin bakar mace.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here