Kishi kumallon mata: Babbar kawarta ta kasheta akan saurayi

0
457

Wata sananniyar mai sayar da gashin mata, mai suna Annishair ta mutu bayan ta ci guba a wani abinci da babbar kawarta ta sanya mata.

A yadda rahoton ya bayyana, kawarta din wacce take da wajen sayar da abinci ita ce take aika mata da abinci, inda a hankali ta dinga sanya mata guba a ciki har sai da taga bayanta, akan saurayi.

Budurwar dai ta mutu kwanaki kadan da suka mutu, inda mutane suka dinga tofin Allah tsine akan wannan kawarta da ta zuba mata gubar.

Wata mai amfani da kafar sadarwa na Twitter mai suna Olly ita ce ta wallafa labarin a shafinta, inda ta ce:

“Wata budurwa da take da wurin sayar da abinci, ita ce take aikowa da babbar kawarta da abinci a kowacce rana, inda ta dinga sanya mata guba a ciki, marigayiyar tana sana’ar sayar da gashi ne na mata, inda ta fara sana’ar a watan Janairu. Kawar ta mutu kwanaki kadan da suka wuce. Kuma ta kasheta ne akan saurayi, wannan wace irin rayuwa ce!”

Ita ma wata mai suna Ego Beke cewa tayi: “An sanyawa Annishair guba, mutane basu da imani.”

Haka ita ma wata mai suna Swarty a shafin na Twitter cewa ta yi: “Wane irin kishi ne da bacin rai a zuciyar mutum da zai sanya shi ya zubawa amininshi guba a abinci.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here