Ki aure ni yanzu ko kuma na nemi wata – Cewar saurayin da budurwarshi tace ya jira Corona ta wuce kafin suyi aure

0
130
  • Wani saurayi ya baiwa budurwarshi wa’adi akan ko ta yarda suyi aure yanzu ko kuma su hakura da auren baki daya
  • Angon ya yanke wannan hukunci ne bayan budurwar tashi ta bukaci ya jira Coronavirus ta wuce domin su sha shagalin biki su more
  • Saurayin ya bayyana cewa alamu na nuni da cewa budurwar tafi damuwa da kawayenta akan maganar aurensu

Wata budurwa da ke shirin yin aure ta bayyana yadda saurayinta ya bata wa’adi akan ko ta yadda suyi aure yanzu ko kuma ta manta da zancen su baki daya, bayan ta bukaci ya jira har lokacin da Coronavirus za ta wuce sai su sha biki.

Amaryar wacce ba a bayyana sunanta ba, ta bayyana haka ga Tima Kumkum, wacce take fitacciyar ma’aikaciya a Hitz FM.

A cewar budurwar ta bayyanawa saurayinta cewa tana so kawayenta da mutane da dama su halarci bikinta, inda take ganin a wannan lokacin da ake ta fama da Coronavirus hakan ba zai yiwu ba.

Dear Tima,My heart just can't take it anymore, we've been dating for 3 years and we decided to get married this year…

Posted by HITZ 103.9 FM on Tuesday, May 12, 2020

A ranar 16 ga watan Maris ne dai, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo, ya sanya dokar hana taron jama’a da ya wuce mutum 25, a kokarin da yake na dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a kasar ta Ghana.

A martanin da ya mayar mata, angon ya bayyana cewa amaryar tafi damuwa da kawayenta fiye da rayuwar auren da za su yi tare da mijinta.

A karshe ya yanke shawarar bata zabi ko ta yarda ayi auren yanzu, ko kuma a mance da maganar auren baki daya.

Mutane da yawa sunyi ta tofa albarkacin bakinsu akan wannan magana. Wata mai suna Daani Enyonam ta tambayi budurwar shin kawayenta za ta aura ko kuwa saurayin, inda ta bayyana mata ta mayar da hankali akan angonta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here