Ke duniya: Fasto ya ajiye kwarangwal din kanwarshi da ta mutu tsawon shekara 10 yana tsafi da ita

0
169

Mutanen unguwar Peace Land, dake Akute cikin jihar Ogun sun shiga tashin hankali, bayan an gano kwarangwal din wata mata a gidan wani babban fasto.

A cewar wanda lamarin ya faru a gabansa, asirin fasto din ya tonu ne, a lokacin da mai gidan da yake haya a ciki yayi kokarin korarsa saboda yaki biyan kudin haya.

“Fasto din yaki biyan kudin haya, tsawon shekara daya kenan, hakan ya saka mai gidan yayi fushi dashi, ya shiga gidan da wasu mutane domin su fitar dashi daga gidan, amma duka sun firgita bayan sunga kwarangwal din matar a dakin shi,”‘ cewar shaidar.

Mutanen yankin duka sunje wajen domin ganewa idonsu abinda ke faruwa, inda cikin gaggawa aka sanar da jami’an hukumar ‘yan sanda.

Sai dai kuma fasto din wanda yake da coci guda a yankin, ya bayyana cewa kwarangwal din na kanwarshi ne wacce ta mutu. A cewarshi, su uku ne a wajen iyayensu – shi da kannanshi mata guda biyu.

Suna zaune a gida daya, sai kwatsam watarana aka nemi daya daga cikin kannan nashi mai suna Funmi aka rasa. Idan mutane suka tambayeshi inda take sai ya ce musu ta shiga cikin daji.

Ashe dai kanwar tashi ta mutu tun shekarar 2010, yana ajiye da gawarta tsawon shekara goma, inda a yadda kwarangwal din ya nuna matar ta mutu tana tsugunne ne.

Tuni ‘yan sanda suka kama shi suka wuce dashi ofishinsu domin cigaba da gabatar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here