Ke duniya: Budurwa ta kashe ‘ya’yanta guda biyu bayan rikici ya hado ta da mahaifiyarta

0
249

Wata mata mai shekaru 24 ‘yar kasar kenya mai suna Winfred Nduku ta cakawa ‘ya’yanta guda biyu wuka a kahon zuci, sannan kuma tayi kokarin kashe kanta bayan rikici ya hado su da mahaifiyarta.

‘Yan sanda sun bayyana cewa lamarin ya faru a gidan mahaifiyartan dake Kayole, cikin birnin Nairobi a ranar Asabar da daddare.

Kakakin rundunar ‘yan sanda dake Kayole, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Kenyans.co.ke, inda ya bayyana cewa Nduku na kwance a asibitin Mama Lucy tana karbar magani.

Da take bayani akan yadda lamarin ya faru, mahaifiyar Nduku, Josephine Wambua cikin kuka ta ce: “Tana zaune a can wajen tana danna waya, sai nace mata ta kula da yaran ta tabbatar sun ci abinci, sannan sai ta koma ta cigaba da danna wayar.

“Sai kawai ta cigaba da danna wayar, na dan jefa mata kofi na kara yi mata magana. Sai ta ce za ta kashe yaran, kawai sai ta dauko wuka ta kashe su,” ta ce.

Bayan ta kashe yaran Nduku tayi kokarin kashe mahaifiyarta, amma bata samu sa’a ba, inda ta yanke ta a hannu yayin da suke ta kokawa.

Nduku tayi kokarin kashe kanta da wukar, inda ta cakawa kanta wukar a ciki, amma anyi gaggawar garzayawa da ita zuwa asibiti ita da ‘ya’yan nata guda biyu, inda suka mutu ana zuwa asibitin.

Shugaban ‘yan sanda na Nairobi Philip Ndolo ya ce an kwantar da Nduku a asibitin Mama Lucy domin ayi mata magani, kuma za a yanke mata hukunci idan ta samu sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here