Ke duniya: Amarya ta bawa saurayi naira miliyan 3 ta roke shi yayi mata cikin shege

0
401

Wani saurayi dan Najeriya mai suna Kosi Ugo ya shawarci maza da su yiwa ‘ya’yansu gwajin DNA, bayan ya bayyana abinda ya faru tsakaninsa da wata sabuwar amarya da tace za ta bashi naira miliyan uku domin yayi mata cikin shege

A cewar Kosi, matar ta sanar da shi cewa bata son ‘ya’yanta suyi kama da mijinta saboda shi gajere ne mai sanko, kuma danginsu suna da tarihi na tabin hankali.

Da yake bayyana lamarin a shafinsa na Facebook, ya ce: “Shekarar da ta gabata matar aure ta bani naira miliyan uku ta roke ni nayi mata cikin shege.

“A cewar ta bata so ‘ya’yanta suyi kama da mijinta, saboda shi gajere ne ga sanko, kuma danginsa suna da tarihin tabin hankali.”

Ya ce “Yaku ‘yan uwa mazaje; naji ance gwajin DNA yanzu ana yin shi daga naira 50,000 zuwa naira 100,000.

“Ba sai ka sanar da matarka abinda zaka yi ba, kawai ka dauki gashin danka ko ‘yarka a lokacin da suke bacci ka kai asibiti.

“Akwai yiwuwar sama da kashi daya cikin biyu na ‘ya’yanku ba naku bane.”

Last year, a newly married woman offered me 3 million naira to impregnate her.According to her, she didn't want her…

Posted by Kosi Ugo on Friday, May 8, 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here