Kayan tallafin abinci da aka kai a rabawa talakawa a Kano sun fara rubewa saboda ruwan sama, yayin da mutane ke zaune cikin yunwa

0
390
Photo Credit: FG palliatives rotting under rain, sun in Kano by Murtala Adewale

Kayan abincin da gwamnatin tarayya ta kai jihar Kano na tallafi da za a rabawa talakawa ya fara rubewa saboda rana da ruwan sama dake dukan shi, cewar jaridar The Guardian.

Mako biyu da suka gabata gwamnatin tarayya ta aika da tirela 110 jihar domin a rabawa talakawa wadanda basu da halin da zasu iya ciyar da kansu a wannan lokaci da aka hana zirga-zirga a jihar.

Ministar jin dadi da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouq ita ce ta bayar da kayan tallafin a ranar 17 ga watan Mayu, 2020.

Kayan tallafin sun hada da ton 5,318 na shinkafa; ton 2,438 na masara; ton 1,380 na gero da kuma ton 900 na dawa.

Abin takaici wannan kayan abinci na miliyoyin nairori an bar su a cikin kamfanin ajiye kayan gona na jihar Kano dake Farm Centre, inda aka bar su a bude ba tare da wani abu da zai hana dukan rana da ruwan sama ba.

Kayan abincin da suke ajiye a wajen tuni ruwan sama wanda aka yi sau uku a jihar ya riga ya jika buhunhunan, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Wata majiya a wajen da tayi nadamar yadda aka bari kayan abincin suka lalace saboda ruwan sama, ta shaidawa jaridar The Guardian cewa, an kwashe sama da mako guda ba tare da anzo an duba halin da kayan abincin ke ciki ba.

“Mutane da yawa na zaune cikin yunwa saboda baza su iya zuwa su samawa kansu abinci da suka saba na yau da kullum ba. Gwamnati ta kawo wannan kayan abinci domin a taimakawa talakawa amma kalli yadda kayan suke a tsakiyar rana ga ruwan sama. Daga yaya mutane na cikin yunwa amma abincin da aka bayar a raba musu yana lalacewa, wannan ba daidai ba ne.”

Lokacin da aka tuntubi shugaban kwamitin bayar da kayan tallafin kuma Mataimakin shugaban Jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Mohammed Yahuza Bello, yayi bayanin cewa za a fara rabawa talakawa kayan abincin da gwamnatin ta bayar daga gobe Alhamis.

Farfesa Bello wanda ya jagoranci raba kayan abincin da gwamnati ta bayar karo na farko, ya bayyana cewa kwamitin na fuskantar kalubale daga wajen gwamnati, amma yanzu komai ya daidaita.

Duk da yake dai kwanakin baya gwamnatin jihar Kano ta raba irin wannan tallafi ga gidaje 50,000 na gundumomin siyasa 484 na jihar.

Kayan tallafin da kwamitin gudanarwa ta COVID-19 take kula da shi, mako biyu da suka gabata ta bayyana cewa za ta kara bawa gidaje 50,000 wannan tallafi a tsakanin kananan hukumomi 44 na jihar domin rage radadin kulle da aka yiwa jama’a saboda cutar coronavirus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here