Katsina: Dan shekara 8 ya mutu bayan kishiyar mahaifiyarsa ta sanya masa guba

0
526

Jami’an ‘yan sanda sun kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Murja Ibrahim, da laifin sanyawa dan gidan kishiyar mai shekaru takwas guba da tayi sanadiyyar mutuwar shi.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah ya fitar, ya ce, a ranar 19 ga watan Yuni, Ibrahim Sani daga kauyen Jidadi dake karamar hukumar Dandume cikin jihar Katsina, ya kawo kara ofishin ‘yan sanda na Dandume, cewar matarshi ta biyu Murja, ta sanyawa dan shi mai shekara takwas, mai suna Habibu Ibrahim.

Isah ya ce jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wajen da lamarin ya faru, inda suka dauki gawar jaririn zuwa asibiti, a can aka tabbatar da cewa yaron ya mutu bayan gabatar da gwaji akan shi.

Kakakin rundunar ya kara da cewa tuni sun cafke mai laifin don gabatar da bincike a kanta.

Haka kuma mun kawo muku rahoton yadda wani miji mai suna Abdulrahman Abdulkadir ya kashe matarsa mai suna Wasila Sada, inda ya jefa gawarta cikin rijiya a jihar ta Katsina.

An ruwaito cewa ya aikata laifin a kauyen Madabu-Dabawa dake karamar hukumar Dutsinma cikin jihar Katsina, a ranar 25 ga wannan watan na Yuni.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here