Kashi 75 na fyade da ake yi a Najeriya Malaman addini ne suke yi – Foluke Daramola

0
717

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, kuma mai rajin kare hakkin wadanda ake yiwa fyade, Foluke Daramola-Salako ta ce kashi 75 na fyade da gidauniyarta take da su duka Malaman addini ne suka yi.

Daramola ta bayyana hakane a wata hira da tayi da mai amfani da kafar sadarwa, Funmi Iyanda.

Jarumar wacce aka yiwa fyade a lokacin da take da shekaru 17 a duniya, ta ce:

“Kashi 75 na fyade da aka kawo mini duka malaman addini ne, kuma a lokuta da dama bama nemowa wadanda aka yiwa fyaden hakkinsu, sai iyayensu su zo su ce mu bar wanda yayi da Allah.”

Daramola ta karyata zargin da ake yi na cewa shigar banza da mata ke yi ne ya jawo ake yi musu fyade.

“Babu abinda yake jawo fyade, alama ce kawai ta son zuciya. Mai yasa suke yiwa yara da tsofaffi fyade, shin wannan ma yana da hadi da shigar banza?

“Da wuya ka samu an yiwa budurwa fyade in dai ba a wajen aiki bane, mafi yawanci anfi yiwa kananan yara da tsofaffi, daga yaya kuma zaku ce mini wai shigar banza ce take jawowa? Mu ba dabbobi bane,” ta ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here