Kashi 50 na bakar fata dake Amurka suna Musulunta saboda ba a nuna banbanci a Islam

0
6259

“Duka mutane asalinsu Adam da Hauwa’u, Balarabe ba shi da wani bambanci da wanda ba Balarabe ba, haka kuma wanda ba Balarabe ba bashi da bambanci da Balarabe,” cewar Annabi Muhammad (SAW).

Wannan Hadisi yana daya daga cikin Hadisai da suka yi suna a kasar Amurka da kasashen Turawa. Kasar Amurka tana da babbar matsala ta nuna bambancin launin fata.

A karni da dama da suka gabata bakar fata na zaune cikin wahala akan wannan nuna bambanci na launin fata, inda har wayau da muke a karni na 21 lamarin bai canja ba.

Kisan bakar fata George Floyd da aka yi a kasar Amurka ya tona asirin kasar, inda duniya ta gane duka irin munafurci da tuggun da kasar take yiwa bakar fata.

Wannan dalili ne ya sanya bakar fata da yawa suke shigowa addinin Musulunci, saboda addinin bai aminta da nuna bambanci ba tsakanin kowacce kabila ko fata.

Wani sabon bincike da kungiyar pewsearch ta gabatar ya nuna cewa kashi daya cikin biyar na mutanen Amurka duk bakar fata ne, kuma duka wadannan bakar fata suna shiga addinin Musulunci ne saboda fama da suke da bambancin launin fata.

Ba wai kuma iya shiga addinin suke kawai ba, suna kuma tabbatar da bin duka ka’idoji wajen tabbatar da zama a addinin.

Shigowar bakar fatan zuwa Musulunci na cigaba da karuwa. Inda suke fita daga wannan matsala ta nuna wariyar launin fata, suke rungumar addinin Musulunci ta hanyar mantawa da tsohon addinin su.

A yau yawan bakar fata dake kasar Amurka ya kai kashi 20 cikin dari, inda kuma kusan kashi 49 cikin dari na wadannan bakar fata duka sun musulunta, kamar yadda binciken ya nuna.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here