Kashe-kashen da ake yi yanzu ya tabbatar da bamu da shugaba a Najeriya – Buba Galadima

0
1897

Babban mai hamayya da gwamnatin shugaba Buhari, kuma dan babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Buba Galadima, yayi bayanin cewa Najeriya ta samu kanta a wani irin yanayi na rashin ingantaccen shugabanci.

Babban dan hamayyar ya ce duba da yadda rashin tsaro yayi kamari a wannan lokaci da ‘yan ta’adda suke cin karensu babu babbaka a Arewacin Najeriya.

Buba Galadima yayi wannan bayani ne a wata hira da yayi da sashen Hausa na gidan rediyon DW dake kasar Jamus.

Ya ce: “Yanzu ka duba abinda ke wakana a ‘Yantumaki, Jibiya, Faskari, Batsari, duba abinda ke faruwa a jihohin Sokoto da Zamfara, tsakani da Allah hakan yana nuni da cewa akwai gwamnati a Najeriya? Ko kuma akwai wanda yake kishin jama’a a Najeriya?

“Ga bashi da aka ciyo masu yawan gaske wanda Allah ne kadai ya san yawanshi, amma babu wani abu guda da gwamnati tayi na azo a gani. Kuma idan mutum yayi magana akan haka sia ace baya son gwamnati.

A daya bangaren kuma Buba Galadima yayi magana akan mulkin tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Sani Abacha, inda ya ce ko hadi babu gwamnatin Abacha ta yiwa ta Buhari fintinkau a fannin sha’ani irin na mulki da kuma ayyuka na cigaban kasa.

Wannan dai duka na zuwa ne sakamakon kashe bayin Allah da aka yi a ‘yan kwanakin nan a jihohin Borno da Katsina.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here