Kasar Saudiyya ta jero sharudda guda 6 da za abi wajen aikin Hajji

0
319

Gwamnatin kasar Saudiyya ta jero sharudda guda shida da mahajjatan da za su samu aikin Hajji a kasar za su bi a wannan shekarar.

Mahukunta a kasar ta Saudiyya ta bayyana cewa sanadiyyar annobar coronavirus, aikin Hajji a wannan shekarar iya mutanen dake cikin kasar Saudiyya ne kawai za su samu halarta.

A wata hira da yayi da manema labarai, ministan lafiya na kasar Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana cewa iya mutanen da suke kasa da shekaru 65 ne kawai za su samu damar halartar aikin.

Haka kuma ya kara da cewa duka mutanen da za su yi aikin Hajjin sai an gabatar da gwajin cutar a gare su kafin a bari su shiga wajen bautar, haka kuma za’a killace su na tsawon mako biyu bayan kammala aikin hajjin.

Haka kuma ministan lafiyar ya bayyana tuni sun dauki matakai da za su tabbatar da cewa wadanda za suyi aikin Hajjin sun bi dokokin da hukumomin lafiya suka gindaya, haka kuma ya bayyana cewa mutanen da za suyi aikin Hajjin ba zai wuce mutum dubu goma ba.

“An tsara asibitoci a wurare daban-daban, koda wani abu na gaggawa zai taso,” ya ce.

“Haka kuma motar daukar marasa za ta dinga bin mahajattan a lokacin da suke gabatar da aikin Hajjin.

“Aikin hajjin za ayi shi lafiya kuma cikin koshin lafiya wannan karon,” ya ce.

Ga dai sharuddan guda shida da ministan lafiyan ya lissafo a kasa:

  1. Mutane da suke sama da shekaru 65 ba za a basu damar yin aikin Hajji ba.
  2. Wadanda suke da rashin lafiya mai tsanani suma ba za a bar su suyi aikin Hajjin ba.
  3. Dole a gwada mutane kafin a bari su fara gabatar da aikin Hajji.
  4. Dole kowa yabi dokar tazara tsakaninsa da sauran mahajjata.
  5. Za a dinga gwada lafiyar mahajjata a kowacce rana.
  6. Za a killace mahajjata na tsawon mako biyu bayan kammala aikin Hajji.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here