Kasar Nijar ta zama kasa ta farko da ta karbi maganin cutar Coronavirus daga kasar Madagascar

0
230

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta karbi tallafin maganin cutar coronavirus daga kasar Madagascar wanda shugaban kasar Andry Rajoelina ya aika da shi.

Daraktan ofishin ministan lafiya na kasar ta Nijar, Isma’il Annar, shi ne ya karbi wannan taimako na maganin wanda kasar ta Madagascar ta aika musu da shi.

Maganin dai ya kasance busashen ganyen wata bishiya ne da ake jikawa a ruwa, domin yiwa masu cutar magani bayan an tabbatar da suna dauke da ita.

Maganin da aka sanyawa suna ‘Covid-Organics’ wani irin tsimi ne da aka samo shi daga wani ganye da aka tabbatar da sahihancinsa wajen maganin zazzabin cizon sauro.

Shugaba Andy Rajoelina na kasar ta Madagascar, shine ya bayyana cewa maganin yana warkar da cutar ta Coronavirus.

Sai dai ya zuwa yanzu masana kimiyya basu tabbatar da ingancin wannan magani ba wajen warkar da wannan cuta ta Coronavirus, kamar dai yadda hukumar lafiya ta duniya ta sanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here