Kasa da mutum 20 ne kacal suka halarci jana’izar Sarkin Rano – Cewar Bashir Ahmad mai taimakawa shugaban kasa

0
314

Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin sadarwa, Bashir Ahmad yayi magana akan wani bidiyo wanda ya nuna mutane masu tarin yawa suna taba gawar wani mutumi a wajen jana’iza.

Wasu masu amfani da kafafen sadarwa sun bayyana cewa an dauki wannan bidiyo ne a wajen jana’izar marigayi Sarkin Rano, wanda ya rasu a jiya bayan an kwantar da shi a asibiti.

Bashir Ahmad wanda yake dan asalin jihar Kano, ya karyata wannan bidiyo, inda ya ce an binne marigayi Sarkin Rano a cikin gidansa awanni kadan bayan rasuwarsa.

Haka kuma mai taimakawa shugaban kasar ya kara da cewa, wani daga cikin manyan masu sarauta a masarautar ta Rano ya bayyana mishi cewa kasa da mutane ashirin ne kacal suka halarci taron jana’izar marigayin.

Ya ce: “An binne gawar Sarkin Rano a cikin fadarsa awa daya bayan mutuwarsa, kuma kasa da mutane 20 ne kacal suka halarci taron jana’izarshi, amma wani bidiyon bogi na mutane masu yawan gaske na ta yawo a kafafen sadarwa a yau, dake nuni da cewa a lokacin jana’izarshi ne, ba haka bane, majiya mai karfi daga masarautar Rano ta sanar dani.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here