Kana taka Allah na tashi: Babban burina na mutu ina da shekara 96 – Cewar Ajimobi da ya mutu jiya

0
404

Mutuwa ita ce karshen kowa, amma ga Isiaka Abiola Ajimobi, rayuwa fiye da shekara 70 a duniya sai da yayi ta a lahira, bayan tsohon gwamnan jihar Oyo ya rasu a jiya Alhamis sakamkon cutar Coronavirus.

Mutuwar ta sa ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ta jiha da ta kasa baki daya take bukatar dattaku da kwarewarsa a siyasa, mutuwar tashi dai ta bawa kowa mamaki.

An ruwaito cewa an kwantar da tsohon gwamnan ne dai a wani babban asibiti dake Legas a ranar 2 ga watan Yuni, amma bai samu sauki daga wannan cuta ba duk da kulawar da ya samu.

A shekarar 2019, a lokacin da ya cika shekara 70 a duniya, tsohon gwamnan yayi magana akan danginsu, inda ya bayyana cewa babu wani a cikin danginsa da ya taba kawowa wannan shekaru na sa ciki kuwa har da mahaifinsa.

Ajimobi, wanda a kwanaki ya ce yana son ya mutu a lokacin da ya cika shekara 70, ya ce ba karamin baiwa bace a gareshi da ya samu ya kai wannan shekaru idan aka yi la’akari da shekarun wadanda suka wuce kafin shi.

“Nagode Allah da ya bani ikon kawowa wannan lokaci, musamman ma a bangaren iyayena babu wanda ya taba kaiwa shekara 70; duka ‘yan uwana maza, ciki harda mahaifina da kakanmu, da dan uwanshi,” cewar Ajimobi.

“Na tabbata abu ne da ya kamata mutum ya godewa Allah, saboda haka ina matukar godiya ga ALlah da ya kawo ni wannan lokaci, saboda ina jina cikin koshin lafiya da farin ciki.

Ajimobi yana da son ya jima a duniya, amma sai dai ance kaddara ta jira fata.

Jim kadan bayan murnar bikin cikar shi shekara 70, Ajimobi na neman kara wasu shekarun domin morewa abubuwan da ya tara a matsayin shi na tsohon dan majalisa, gwamna kuma hamshakin mai kudi. Amma ance kana taka Allah na tashi.

A wata hira da yayi da Tribune, tsohon gwamnan ya bayyana duka burinshi na rayuwa kafin ya mutu.

“Yan Najeriya da yawa suna kaiwa shekaru 96 100 wani lokacin, suna shiga wani hali. Ina ganin zan iya rayuwa zuwa wannan shekarun. Haka na yadda dashi kawai: Babu wani tabbatacen al’amari game da hakan, wani lokacin abinda ka yarda dashi na iya faruwa.”

Amma sai gashin wannan mafarki nashi bai tabbata ba, saboda ya koma ga mahaliccinshi, a asibitin jihar Legas, a cewar wasu kafafen sadarwa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here