Kaji tsiyar selfie: Kada ya cinye budurwa yayin da take kokarin daukar selfie da shi

0
206

Kada ya kashe wata budurwa a lokacin da take kokarin taba shi ta dauki hoton selfie dashi bayan ta ganshi a cikin gulbi, cewar mahukunta.

Matar mai suna Cynthia Covert, mai shekaru 58 ta kai ziyara gidan kawarta dake tsibirin Kiawah, yankin kudancin Carolina, domin tayi mata gyaran farce, kamar yadda ‘yan sanda suka ruwaito.

“A duk lokacin da Covert ta zo tana nuna kamun kai, amma yau lamarin ya bambanta, domin tana ta murna cewa saurayinta zai zo Tennessee ya kawo mata ziyara,” cewar kawar.

Kamar yadda The Post da kuma Courier suka ruwaito. Ms Covert ta sha giya kadan a lokacin da take tare dasu, amma basu sani ba ko tasha wani abu daban ba banda giyar.

Suna zaune a wajen gyaran farcen sai Ms Covert ta hango kada a cikin gulbi, cikin farin ciki ta tunkari inda yake.

Taje har wajen da kadan yake a cikin gulbin sai ta fara daukar hotuna tare da kadan, inda ita kuma kawarta tana yi mata gargadi akan yadda taga kadan ya cinye wata barewa a wannan wuri da take daukar hoton shi.

“Banyi kama da barewa ba.” Martanin Ms Covert kenan, inda daga nan taje ta nemi taba kadar.

Ai kuwa ba makawa kadar ta kama mata kafa ta ja ta cikin ruwan gulbin.

“Ba zan kara ba daga yau,” abinda aka ji Ms Covert na cewa kenan bayan kadar ta ja ta cikin ruwan, cewar jami’an hukumar ‘yan sanda.

Mijin kawarta da makwabta su suka yi kokarin fito da ita daga cikin gulbin bayan sun sanya mata igiya. Amma sai kadar tayi tsalle ta kara dannata cikin ruwan.

Jami’an tsaro da dama sun halarci wajen, inda suka fara neman gawar matar na tsawon mintuna 15, inda a karshe suka gano gawarta, amma duk da haka kadar na rike da kafar matar.

Daya daga cikin ‘yan sandan da suka halarci wajen ya harbi kadar da bindiga, inda suka samu ta saki Ms Covert, inda kadar ta mutu.

Daga baya jami’an ‘yan sandan sun bayyana cewa Ms Covert ta mutu ne sanadiyyar ruwan da ta sha a lokacin artabu da kadar, Ms Covert ce mutum ta uku da kada ta kashe a jihar ta Carolina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here