Kaduna: Karti 4 sun yiwa ‘yar shekara 13 fyade a lokaci daya bayan sun bugar da ita da kwaya

0
534

Wasu mutane guda hudu sun yiwa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade a jihar Kaduna, bayan sun bata kwaya ta sha ta bugu, inda suka ajiye ta a kasan wata mota a kusa da gidansu bayan sun gama amfani da ita.

Ma’aikatar ayyukan jin kai da cigaban al’umma ta jihar ita ce ta bayyana haka a ranar Alhamis.

Ma’aikatar ta ce tuni ta fara gabatar da bincike akan wannan lamari.

Ta ce mutanen sun dauki yarinyar akan babur inda suka jefar da ita a kasan wata mota da take ajiye a kusa da gidansu bayan sun gama amfani da ita.

Ma’aikatar ta bayyana hakane a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, inda ta ce bayan shafe sa’o’i ana nemanta a karshe an gano inda take inda aka yi gaggawar garzayawa da ita asibiti.

Haka ta kara da cewa an kama mutane hudun da suka yi mata fyaden da kuma wani da ya taimaka musu, kuma tuni an mika lamarin na su ga hukumar ‘yan sanda ta CID.

Ma’aikatar ta ce bayan hukumar ‘yan sandan ta gama bincike, za a mika su gaban kotu domin yanke musu hukunci daidai da laifin su.

Ta kara da cewa duk kace-nace da ake a shafukan sadarwa akan matsalar fyade a Najeriya, mutanen banzan sun ki saurarawa da wannan mummunar al’ada ta su.

Daily Trust ta ruwaito cewa ana ta gabatar da zanga-zanga a shafukan sadarwa akan gwamnati ta dauki mummunan mataki akan masu yiwa mutane fyade.

Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan yankewa wani mutumi da ya yiwa wata yarinya ‘yar shekara biyu fyade hukuncin kisa a jihar ta Kaduna.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here