Ka canja hafsoshin tsaron ka – Masana sun shawarci Buhari

0
389

A jiya Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hafsoshin tsaronsa cewa su kara kaimi wajen aikin da suke yi na kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Wasu masana a fannin tsaro sun bayyanawa Daily Trust cewa basu ji dadi ba ko kadan, inda suka bukaci shugaban kasar ya kori duka hafsoshin tsaron Najeriya, ya canja tsarin tsaron kasar sannan ya sanya wasu sababbi domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar.

Shugaban kasar ya ce ba zai sake karbar wani uzuri daga wajen hafsoshin na shi ba, inda ya ce ba zai kara yi musu magana ba, amma ya rage nasu suyi duk abinda ya kamata wajen kawo karshen wannan matsala a Najeriya.

Duk da dai wakilin shi ne yake magana da bakin shi, amma wannan shine karo na farko da shugaban kasar ya kira hafsoshin tsaron nasa tun bayan nada su a ranar 13 ga watan Yulin shekarar 2015.

Yana basu umarnin a koda yaushe, sannan yana sake sabunta aikinsu a ofis sau da dama duk kuwa da matsalolin da ake samu saboda matsalar tsaro.

Mai bada shawara a fannin tsaro na gwamnatin tarayya, Manjo Janar Babagana Monguno, shine yayi magana a madadin shugaban kasar, a lokacin da yake hira da manema labarai na fadar shugaban kasar akan abubuwan da aka tattauna a wannan taro da suka yi da shugaban kasar.

Monguno ya samu rakiyar daraktan tsaro na sirri (DDI), AVM Mohammed Sani Usman, da darakta janar na ‘yan sandan farin kaya (DSS), Alhaji Yusuf Magaji Bichi.

Hafsoshin tsaron sun hada da: Babban hafsan tsaro na kasa (CDS), Janar Gabriel Olonisakin; Babban hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas; Babban hafsan sojan sama, Air Marshal Sadique Abubakar; sai kuma Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

Da yake tsokaci akan sabon umarnin da Buhari ya bawa shugabannin tsaron, kwararre akan harkar tsaro kuma masani a fannin ‘yan ta’adda, Dakta Amaechi Nwaokolo, ya ce lokaci yayi da shugaban kasar zai fara aiki ba tare da bayar da umarni ko gargadi ba.

Da yake jaddada cewa hafsoshin tsaron sun wuce lokacin aikinsu, Nwaokolo ya ce: “Mun gaji da duk wadancan ka’idojin na baya, wadanda basu haifar mana da komai ba. Ya kamata shugaban kasa yayi abinda ya kamata saboda lokaci yayi da wadannan hafsoshin sojin za su tafi.”

“Sun riga sun gaji, Kamata yayi a sauke musu nauyin dake kansu. Sun yi iya bakin kokarinsu abin yaki yiwuwa. Maganar gargadi duka bata taso ba, domin kuwa babu wani canji da za ta kawo. Muna da mutanen da a shirye suke suyi wannan aiki,” cewar Amaechi.

Haka shi ma Salihu Bakhari, tsohon ma’aikacin soja, wanda yayi aiki a wurare daban-daban na Najeriya, ya ce lokaci yayi da Buhari zai saurari al’umma. “Wannan gargadi zai kai har karshen shekarar 2023. Mai yasa ba zaka basu lokaci ba? Idan har basu yi abinda ya kamata a cikin wannan lokaci ba ka kore su.

“Kashe-kashen yayi yawa, mutane har sun fara zanga-zanga amma yayi buris yayi kunnen uwar shegu; dama abinda ya fada jiya kowa yasan hakane.

“An ajiye sojoji a jihohin Zamfara da Katsina sama da watanni biyu kenan amma har yanzu babu wani sakamako.

A bangaren yadda za a karfafawa sojojin guiwa wajen yin aiki, Bakhari ya ce: “Sojojin za su samu karfin guiwa ne kawai idan an basu kayan aikin da suka dace kamar yadda ya faru a shekarar 2014, lokacin da aka kawo sababin kayan aiki komai ya canja daga kananan hukumomi 35 dake cikin jihohi uku dake hannun Boko Haram a yankin arewa maso gabas zuwa karamar hukuma 1, kafin a bayar da mulki a shekarar 2015.

“Abu na biyu shine cire hafsosin tsaro na kasa, saboda yanzu haka duka jami’an tsaro da suke kasa sun cire rai da shugabantar hukumomin. Babu wani abu sabo da wani daga cikinsu zai kawo wanda ba a kawo ba a shekaru biyar da suka wuce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here