Jonathan na tsaka mai wuya yayin da gwamnatin tarayya ta sako shi gaba kan kudaden shi na kasar waje

0
145

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa bashi da kadarori ko kudade a kasashen ketare.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Ikechukwu Eze, ya fitar akan kokarin da gwamnatin tarayya take na bincike akan asusun bankuna na tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da matarsa, Patience Jonathan.

“Hankalin mu yazo kan rahotannin da muka yi ta gani a kafafen sadarwa na cewa gwamnatin tarayya ta fara bincike akan kudaden tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da matarsa, Dame Patience Jonathan a kasar Amurka,” cewar Mr Eze.

“Sai dai kuma mun san gwamnatin tarayya ba ta tuntubi tsohon shugaban kasar ko matarsa akan wannan lamari ba kafin ta fara wannan binciken, da ace sun tuntube su da mun sanar da su cewa kada ma su fara bincike akan abinda babu shi.

“Za kuma tunatar da jama’a, a ranar 5 ga watan Maris shekarar 2014, lokacin da za a rantsar da ministoci, a lokacin tsohon shugaban kasa Jonathan, ya ce ‘ina matukar kishin ‘yan Najeriya, bani da kadarori ko kudade a kasar waje.”

Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa a wannan lokacin Jonathan ya bayyana cewa bashi da kudade a kasashen ketare, kuma har ya zuwa yanzu babu abinda ya canja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here