Jerin manyan Kabilu guda 10 a nahiyar Afrika da suka fi yawan al’umma

1
895

Afrika nahiya ce mai albarka da Allah ya albarka ce ta da kabilu kala daban-daban. Press Lives za ta kawo muku jerin manyan kabilun nahiyar Afrika.

Ga jerin manyan kabilun guda goma da suka fi yawan al’umma a fadin nahiyar Afrika.

1. Hausa – miliyan 78

Kabilar Hausa tana da yawan al’umma miliyan 78 a cikin kasashen dake fadin nahiyar Afrika.

2. Igbo – miliyan 45

Da yawan mutane miliyan 45, kabilar Igbo sun zama na biyu a cikin jerin kabilun da suka fi yawa a nahiyar Afrika.

3. Yoruba – miliyan 44

Kabilar dake bin bayan kabilar Igbo ita ce kabilar Yoruba, wacce ke da yawan mutane miliyan 44.

4. Oromo – miliyan 40

Kabilar Oromo suna da yawan mutane miliyan 40 a nahiyar Afrika baki daya.

5. Fulani – miliyan 35

Kabilar Fulani suna da mutane miliyan 35, hakan ya mayar da ita kabila ta biyar a yawan mutane a nahiyar Afrika.

6. Amhara – miliyan 20.2

Kabila ta shida da tafi al’umma a Afrika ita ce kabilar Amhara.

7. Akan – miliyan 20

Kabilar Akan ita ce kabila ta bakwai da tafi yawan al’umma a nahiyar Afrika

8. Somali – miliyan 20

Wacce ke bin bayan kabilar Akan ita ce kabilar Somali, wacce ita ma take da mutane miliyan 20.

9. Hutu – miliyan 18.5

Kabila ta tara ita ce kabilar Hutu, da yawan al’umma miliyan 18.5.

10. Ijaw – miliyan 15

Kabilar Ijaw ita ce kabila ta goma a cikin jerin kabilu mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika, inda take da yawan mutane miliyan 15.

A labari makamancin haka kuma, akwai wani gamsashen bayani game da kabilar Hausa. Kabilar Hausa ita ce kabila mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika wacce ke da yawan mutane miliyan 78.

Yaren Hausa kuma shine yare na biyu da yafi rinjaye a nahiyar Afrika, inda yawan mutane dake yaren suka kai mutane miliyan 120.

Mutanen dake yaren suna zaune a kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, Benin, Cameroon, Togo, Central African Republic, Ghana, Sudan, Eritrea, Equatorial Guinea, Gabon, Senegal, Gambia da dai sauran su.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here