Jerin laifuka 11 da ake zargin Magu da su

0
550

A ranar Litinin ne dai, mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ya ba da shaida a gaban kwamitin dake duba akan zargin da ministan shari’a Abubakar Malami (SAN), yake yi masa.

Kotun wacce tsohon shugaban kotun daukaka kara, Alkali Isa Ayo Salami, ya jagoranta.

An tsare Magu a daren jiya bayan amsa tambayoyi a gaban kotun.

An fita da shi daga Villa, inda jami’an hukumar FCID, suka yi masa tambayoyi da misalin karfe 10:15, jim kadan bayan kwamitin ta gama zamanta.

An ruwaito cewa jim kadan bayan kammala zaman, an raka Magu cikin wata farar mota mai kirar Hilux da aka sanya mata lamba 371D.

Haka kuma an gano cewa akwai yiwuwar an dakatar da Magu daga aiki, saboda hana shi shiga ofishin shi da aka yi.

Wata majiya ta ce: “Akwai yiwuwar fadar shugaban kasa tuni ta gama shirin maye gurbin shi da wani wanda ya dace.”

Wani bincike da wakilin The Nation Online yayi, ya bayyana wasu daga cikin zargin da Malami yake yiwa Magu.

Wasu daga cikin zargi 22 da ake yiwa Magu din sun hada da:

 1. Zargin samun bambance-bambance a cikin bayanan da EFCC da ma’aikatar kudi ta tarayya suka bayar akan kudaden da aka kwato.
 2. Samun biliyan 539 a matsayin kudaden da aka kwato maimakon biliyan 504 da aka yi ikirari a baya.
 3. Kin bin dokar ofishin AGF a wasu hukunce-hukunce da yake bayarwa.
 4. Rashin isassun hujjoji kan korar karar tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison Madueke.
 5. Jinkiri wajen binciken kan tsarin cigaban masana’antu wanda ya haifar da sabani.
 6. Rashin mutunta umarnin kotu akan sakin naira biliyan 7 a madadin tsohon daraktan bankin First Bank.
 7. Zargin jinkiri wajen daukar mataki akan jiragen ruwa guda biyu da sojojin ruwan Najeriya suka kama wanda ya haifar da asarar danyen mai.
 8. Zargin daga kafa da wasu masu bincike suka yi da ake kiransu da yaran Magu.
 9. Kai karar wasu alkalai zuwa ga shugabanninsu ba tare da tuntubar AGF ba.
 10. Zargin sayar da kadarorin da aka kwace ga abokanan aiki da kuma abokai.
 11. Zargin bada umarnin bincike kan wasu kafafon watsa labarai.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here