Jerin kasashen Afrika guda 10 da ba a dauke musu wutar lantarki

1
2594

Shafin Twitter na Africa Fact Zone ya sake wallafa wata kididdiga da ta shafi yankin na Afrika. A wannan karon shafin ya binciko jerin kasashen Afrika guda goma da ba a dauke musu wuta.

A cikin jerin kasashen kasar Mauritius, da Tanzania su ne suka zo a matsayin na daya dana biyu kuma suke da wutar lantarki dari bisa dari.

Kasar Egypt, Algeria, Morocco da Seychelles, sune suka zo a na 99.8%, 99.1% da kuma 99%.

Babu wata kasa a cikin jerin kasashen da take da kasa da 80%, inda kasar Ghana da South Africa suka zo na 9 dana 10, da 84.3% da kuma 84.2%.

Ga dai jerin kasashen a kasa:

  1. Mauritius (100%)
  2. Tunisia (100%)
  3. Egypt (99.8%)
  4. Algeria (99.1%)
  5. Morocco (99%)
  6. Seychelles (99%)
  7. Cape Varde (96.1%)
  8. Gabon (90.7%)
  9. Ghana (84.3%)
  10. South Africa (84.2%)

Idan ba a manta ba a kwanakin baya Press Lives ta kawo muku rahoton yadda shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana kudurin karbo wutar lantarki daga wajen ‘yan kasuwa.

Sanatan ya bayyana cewa bai ga amfanin tura musu makudan kudade da gwamnatin tarayya take yi ba alhalin babu wani canji da ake samu daga wajen su.

Ya ce matukar kasar za ta cigaba da bin ta ‘yan kasuwa to za a shafe nan da shekaru 10 ba tare da an samu cikakkiyar wutar lantarki ba.

Ga dai rahoton dalla-dalla: Lokaci yayi da zamu karbo wutar lantarki daga hannun ‘yan kasuwa – Sanata Ahmad Lawan

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here