Jerin jihohin da suka ki amincewa da dokar gwamnatin tarayya ta bude Masallatai da Coci

0
628

Akasin yadda mutane suka ji na cire dokar hana zuwa wuraren ibada da gwamnatin tarayya, ran mutane da dama ba zai yi dadi ba a wasu jihohin kasar yayin da wasu gwamnonin suka nuna cewar baza su cire wannan doka ba.

Gwamnatin tarayya dai ta sanya dokar hana taron mutane da yawa, inda kuma ta bude wuraren bauta a kokarin da take yi na dakile yaduwar cutar coronavirus a fadin kasar.

Amma bayan sanarwar da kwamitin gudanarwa ta cutar COVID-19 ta fitar, ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta cire dokar hana zuwa wuraren ibada a Najeriya baki daya, inda dokar ta fara aiki a ranar 1 ga watan Yunin nan.

Haka kuma kwamitin ta bayyana cewa gwamnatin ta amince da wannan doka ne a bisa sharadin dole masu ibada za su bi dokokin da kwamitin da kuma gwamnonin jihohi suka sanya a kansu.

Sai dai kuma, gwamnonin wasu jihohin a Najeriya sun ce babu makawa wuraren ibada za su cigaba da zama a kulle.

Ya zuwa yanzu dai akwai sama da mutane 10,819 da suka kamu da cutar a Najeriya, inda mutane 3,239 suka warke, mutum 314 kuma suka riga mu gidan gaskiya.

Wannan dalilin ne ya sanya Press Lives ta nemo muku jerin jihohin da suka ki amincewa dokar ta gwamnatin tarayya ta bude wuraren ibadar.

1. Lagos

Ko musu babu kowa ya san cewa jihar Legas ita ce jihar da tafi kowacce yawan masu cutar coronavirus a Najeriya, inda take da kimanin mutane 6,000 da suka kamu da cutar da kuma mutum 67 da suka mutu a jihar sanadiyyar cutar.

Jim kadan bayan sanarwar gwamnatin tarayya akan bude wuraren ibadar, kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Legas, Anofiu Elegushi, ya fito ya bayyana cewa jihar ta Legas za ta cigaba da zama a rufe, ma’ana babu zuwa wuraren ibada.

2. Kaduna

Jihar Kaduna dake da mutane 297 ta zama jiha ta bakwai da tafi yawan masu cutar. Inda ita ma a martanin da gwamnatin jihar ta mayarwa da gwamnatin tarayya a ranar Litinin, ta ce ba za ta bude kasuwanni da wuraren bauta ba.

Wannan sanarwa ta fito dauke da sa hannun mai taimakawa gwamnan jihar a fannin sadarwa, Muyiwa Adekeye, a ranar Talata, 2 ga watan Yuni.

3. Kwara

A matsayin jiha ta 15 da suke da mafi yawan masu cutar, jihar Kwara tana daya daga cikin jihohin Najeriya da annobar ta harba.

Gwamnatin jihar ita ma ta nuna rashin yiwuwar bude Masallatai da Coci a fadin jihar. Kwamishinan lafiya na jihar, Raji Abdulrazaq shine ya bayyana haka, inda yace duk da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin bude wuraren bautar, yanzu ya rage ga gwamnatocin jihohi su yanke nasu hukuncin.

4. Osun

Haka ita ma gwamnatin jihar Osun, a na ta bangaren, ta ce gwamnati za ta kira shugabannin addinai don tattaunawa akan wannan lamari.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da gwamnatin tarayya tuni ta fitar da ka’idojin da ya kamata mutane su bi domin cigaba da yin ibada a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here