Jerin jihohi guda 5 da gwamnatin tarayya za ta bawa naira biliyan 148 na gyaran hanya

0
809

Majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya ta amince da biyan kudaden da wasu jihohi suka kashe wajen gina hanyoyin gwamnatin tarayya.

Yawan kudin da za a mayarwa jihohin guda biyar kai N148,141,987,161.25.

Ga jerin jihohin guda biyar da za su more da wadannan makudan kudade:

  1. Jihar Cross Rivers – N18,394,737,608.85
  2. Jihar Ondo – N7,822,147,577.08
  3. Jihar Osun – N2,468,938,876.78
  4. Jihar Bayelsa – N38,040,564,783.40
  5. Jihar Rivers – N78,953,067,518.29

A rahoton da Sahara Reporters ta fitar, ministan ayyuka da gidaje na tarayya ya gabatar da wata takarda a lokacin taron da majalisar zartarwar ta gabatar ga shugaba Buhari a ranar 3 ga watan Yuni.

Legit.ng ta ruwaito cewa ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, wanda ya wakilci ministan ayyukan da gidaje Fashola, ya ce majalisar tayi gargadin cewa daga yanzu babu wata jiha da za a sake mayarwa da kudi idan tayi aiki ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here