Jerin abubuwa guda 8 da ya kamata kowa ya sani wadanda basa karya azumi

0
137

A kowanne watan Ramadana Musulmai da yawa suna tambaya akan abubuwa da dama da suke tunanin suna karya azumi. Azumi na da matukar muhimmanci ga Musulmai shi yasa kowa ya kamata ya san da wadannan abubuwa.

Kamar yadda kwamitin binciken addinin Islama ta Majmooh Al-Fatawaa ta Shehun Malami Ibn Baz da kuma Fatawaa Ramadana ta Ibn Al-Uthaymeen, su suka bayar da wannan Fatawaaa.

1. Habo

Baya karya azumi tunda ba wai ana yin shi da gangan bane.

2. Gwajin jini

Baya karya azumi, in dai ba wai an karawa mutum jini mai yawa bane.

3. Cire hakori

Baya karya azumi, sai dai idan jini ya fita da yawa da zai iya cika kofi.

4. Wanke baki da man wanke baki

Baya karya azumi, sai idan an hadiye man wanke bakin da gangan da ganganci.

5. Maganin ciwon ido ko na kunne

Babu wata doka da ta nuna yana karya azumi.

6. Kwallin ido (Kajal)

Shi ma baya karya azumi.

7. Maganin Asma

Maganin asma baya karya azumi, kamar yadda babu inda hakan ya nuna.

8. Turare

Turare ma baya karya azumi kamar yadda fatawar Malaman ta nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here