Malaika Arora ta wallafa binciken da tayi akan muhimmiyar hanya da ake bi wajen shan ruwa. A ‘yan kwanakin nan ta sake wallafa wani sirri na shan ruwa a shafinta na sadarwa.

Taurari da suke nuni da yadda ake tafiyar da rayuwa, ya cancanci a yaba musu. Malaika Arora Khan, ta wallafa wannan sirri da ta samo a shafinta na Instagram, wanda take da mabiya miliyan 11.2. Ta bayyana cewa muna kokari kullum wajen ganin lafiyar jikinmu, a yayin da mutane da yawa suka manta da muhimman hanyoyin.

Wadannan ka’idoji sun hada da yadda muke shan ruwa. Yadda ake shan ruwa da hanyar da ta dace, wanda bamu damu bin dokokin ba. Malaika ta bada shawarar yadda za a bi wannan ka’ida cikin sauki.

Duk da dai muna jinjina mata game da bidiyo, jarumar mai shekaru 46 ta ce tayi dan karamin bincike akan hakan. Ta wallafa bidiyon, inda take cewa hanya mafi kyau ta shan ruwa ita ce a zaune a kuma dinga sha a hankali, ba wai a tsaya a kwankwada ba.

A gefe guda kuma, addinmu yayi mana nuni akan wanna hanya ta shan ruwa, tun shekaru masu yawan gaske, inda ya nuna mana hakan ita ce hanya mafi dacewa.

Haka kuma a bangaren kimiyya, duniyar kimiyya ta bayyana hakan a matsayin hanya mafi kyau da lafiya wajen shan ruwa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here