Jaruma tayi nadamar abinda tayi, ta nemi afuwar Hausawa da Musulmai da tace su daina bin shafinta

1
381

Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa ya nuna fitacciyar matar nan da tayi suna a Najeriya wajen bada shawarwari akan zamantakewar aure, wato Jaruma Empire.

Jaruma dai ta dauki bidiyon ne da kanta inda take rokar Musulmai Hausawa ‘yan arewa akan su yafe mata tayi nadamar abinda tayi a baya na cewa su daina bin shafinta na Instagram.

Ta ce yanzu da ta samu mabiya miliyan daya a shafinta na Instagram, za ta mayar da hankali wajen magana akan auren mata da yawa, da zama da dangin miji, dangin amarya, ‘ya’yan uba da sauransu.

Ta ce ta san wannan matsalar tafi shafar Musulmai ‘yan arewa hakan ya sanya za ta bawa fannin muhimmanci.

“Hauwa Musulmai ‘yan arewa na ce ku daina bin shafina a shekarar 2018, dan Allah ku yafe mini, yanzu kwana hudu kenan ina fada na samu mabiya miliyan daya.

“Ina so na cigaba da magana akan auren mata da yawa, zama da dangin miji, zama da dangin mata, kishiya, ‘ya’yan kishiya da sauransu, kuma na san wannan yafi shafar Musulmai ‘yan arewa.

“Dan Allah Musulmai Hausa kuyi hakuri akan maganar da nayi a baya.”

Video Source: Tashar Tsakar Gida

Idan ba a manta a shekarar 2018, Jaruma ta fito a wani bidiyo inda ta dinga yiwa Hausawa ‘yan arewa gargadi akan kada su sake bin shafinta, inda ta ce Hausawa basa yiwa mutum murna idan abin alkhairi ya same shi.

Ta ce babu abinda Hausawa suka sani sai suga mutum ya samu ci baya a rayuwa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here