Fitaccen dan wasan barkwancin nan na kudancin Najeriya, John Okafor wanda aka fi sani da Mr Ibu, yana bangaren masu ra’ayin cewa basu yadda da cutar covid-19 a Najeriya ba, wacce ke kashe al’umma a fadin duniya.

A wata hira da yayi da The Nation, fitaccen jarumin ya ce bai yadda wannan cuta ta wanzu a Najeriya ba, saboda haka shi bai dorawa kansh wata damuwa kan cutar ba. A cewar shi har yanzu bai san wani wanda ya kamu da cutar ko ya mutu sanadiyyar cutar ba.

“Najeriya bai kamata mu sanya kanmu a cikin wannan lamari na cutar COVID-19, ban ga dalilin da zai saka mu damu da ita ba. Iya ‘yan Najeriya dake kasashen ketare ne kawai za su damu da wannan cutar.

“Babu cutar COVID-19 a Najeriya, kuma ban damu ba. Daga yaya China za ta kirkiri cuta, ita kuma Amurka ta fara sayarwa da kasashen duniya, sannan kuma kawai sai mutane su fara mutuwa saboda sun san tana kisa. Mun gode Allah muna da yanayin zafi, ita kanta cutar tana jin tsoron mu.

“Bana jin tsoron komai, ina saka kayana ne na fita nayi yawona. Babu komai a Najeriya, babu wanda ya mutu a wannan yankin, idan kaje wani yankin ma kuma babu wanda ya mutu, kaje filin wasa nan ma babu wanda ya mutu.

“Ina sanar da kowa ba wai iya gwamnati ba, ku dinga fadar iya abinda kuka sani ku daina kara gishiri. Mu muke kirawa kanmu cutar da kanmu, Cuta tana wucewa da kanta, amma mu ‘yan Najeriya mu muke kara kiranta. Baza kaga COVID-19 ba saboda babu ita a nan.”

Dangane da kara samun yawaitar masu cutar da hukumar NCDC take bayyanawa, Mr Ibu ya ce:

“Shin kun san wani mai ita?

“Ka taba zuwa wajen jana’iza ance maka cutar ce ta kashe mamacin? Ka taba zuwa asibiti an sanar da kai cewa wannan mutumin cutar COVID-19 ce da shi? Ka taba ganin dangi da suka ce ga wani dan uwansu da COVID-19 ta kashe? Babu, kullum su suke fada kuma kullum sai kaji sun fada. Ita kanta cutar tsoron mu take yi.

“Idan har mutane ne wadanda cutar ta kashe, su kawo mana hoton mutum daya wanda wannan cutar ta kashe, mu kuma zamu nemo dangin wannan mutumi.

“Babu wannan cutar a Najeriya, muna da yanayi mai zafi, cutar tsoron mu take ji kamar yadda muke jin tsoronta, saboda haka baza ta wurin mu ba.

“Ta shafi kamfanoni da dama a kasar nan, ta hana mu fita aiki saboda karya da munafurci. Abu kadan ya rage yunwa ta kashe ni, badan cewa akwai mutanen kirki da suke bamu kudi ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here