Irin tashin hankalin dana shiga bayan na kamu da Coronavirus na kuma gogawa ‘yata – Rahma Abdullahi

0
465

Sakatariyar majalisar karamar hukumar Abuja, Rahma Abdullahi, ta bayyana cewa ta kamu da cutar coronavirus a wajen aiki, kuma ta gogawa ‘yarta.

Ta ce ta shiga tashin hankali da ciwo wanda ba za ta iya misaltawa ba.

Sai dai cikin ikon Allah duka ‘ya da uwar sun samu lafiya duka sun dawo gida lafiya lau.

Ta ce: “Na dauki cutar COVID-19 a kokarin da nake na yin aiki, kuma na gogawa diyata. Ciwon da tashin hankalin dana shiga ba zai iya misaltuwa ba. Yau ni da diyata abar kaunata mun dawo gida lafiya lau. Nagode Allah, kuma nagode muku da soyayyarku da kuma addu’o’inku. Mun fi karfin coronavirus.”

Yayin da wani mai suna @Horlufemi yayi mata sharhi da cewa zazzabin cizon sauro ne ya kamata. Sannan ya tambayeta akan nawa aka biya ta hado wannan karya. Rahama ta ce yanzu babban abinda take buri shine tayi kokarin wayar da kawunan miliyoyin ‘yan Najeriya akan yaduwar cutar. Inda ta ce cutar gaskiya ce ba karya ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here