Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: ‘Yan Shi’a sun tone kabarin Umar bin Abdul’aziz jika a wajen Sayyadina Umar (RA)

2
12478

‘Yan Shi’a tare da hadin guiwar Iran da Bashar Al-Assad sun tone kabarin Khalifa Umar bin Abdul’Aziz, wanda yake jika ne a wajen Sahabin Manzon Allah (SAW) na biyu, wato Sayyadina Umar bin Khattab (RA).

‘Yan Shi’ar sun tone kabarin a garin Dier Sharqi kusa da Maarat Al-Numan dake Idlib kasar Syria, inda suka dauke sauran abin da ya rage daga cikin kasusuwan shi a cikin kabarin.

Lamarin dai ya yadu ne bayan wani shafi na Twitter ya wallafa bidiyon lokacin da ‘yan shi’ar suka bude kabarin suke fito da kasusuwan shi. Bidiyon ya nuna kabarin Khalifan tare dana matarshi da kuma sauran mutane lokacin da suka bude.

‘Yan ta’addar Shi’a din sun kwace garin a cikin watan Fabrairun wannan shekarar, inda suka kone inda kabarin yake baki daya.

Wannan abu da ‘yan Shi’ar suka yi ya sanya bacin rai sosai ga ‘yan Sunni wadanda suka yarda cewa Umar bin Abdul’aziz shima Khalifa ne kamar sauran Khalifofi.

Yana da matukar muhimmanci da girma a wajen ‘yan Sunni saboda yadda ya tafiyar da mulkinsa cikin adalci da kuma bin dokokin Al-Qur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma shi jikane daga cikin jikokin Sahabin Manzon Allah (SAW), Umar bin Khattab (RA), wanda yayi suna matuka a Musulunci, kuma shine Sahabin Manzon Allah na biyu bayan Abubakar (RA).

Umar bin Abdul’aziz yayi mulki na tsawon shekara biyu da watanni biyar a farkon karni na takwas.

‘Yan Shi’a dai sun jima suna tone kabarurrukan ‘yan Sunni. Kwanan nan ‘yan Shi’ar wadanda suke bin bayan Iran da Assad suka tone kaburburan wasu manyan Malamai, Shugabanni na Sunni.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here