Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Yadda wata mata mai suna Hauwa ta binne jarinta da rai a Kaduna

0
368

A wani rahoto da muke samu, wata mata mai shekaru 33 a duniya mai suna Hauwa, ta hada baki da yayarta mai shekaru 35 mai suna Zainab, suka ciro jaririn dake cikinta suka binne shi da rai a wani Otel da ake kira da People’s Club Hotel dake Tudun Wada, Kaduna.

Bincike ya bayyana cewa duka ‘yan uwan da suke zaune a kusa da otel din sun kama daki ranar Juma’a da daddare, inda suka biya naira dubu biyu kudin daki.

Wata majiya dake a yankin ta tabbatar da cewa kowa ya san budurwar a yankin, duk da dai ba za su iya bayyana ko cikin na wata nawa ne ba, sai dai akwai yiwuwar ta aikata hakan ne saboda jaririn ba shi da uba ko kuma takura da danginta suka sanya mata.

‘Kowa ya san Hauwa tana da ciki a nan yankin, ta zo jiya ta kama daki. Babu wanda ya san cewa ga abinda take kokarin yi. Abinda bamu sani ba shine, ko ta haifi jaririn ne kafin gari ya waye ko kuwa wani ne ya taimaka mata aka ciro jaririn daga cikinta,” cewar wanda lamarin ya faru a gabansa.

“Yau da safe, wani ma’aikacin otel din ya gano su ita da yayarta suna haka kabarin da suka binne jaririn. Abin babu dadin ji.”

Wani wanda ya gano su da idonshi mai suna Bello Abdulmumin, ya ce: “Kawai na zo naga matan guda biyu da misalin karfe 11 na rana suna haka rami a can wurin (ya nuna wajen da hannunsa).

“Bayan sun gama haka sai suka sanya wani abu a ciki suka rufe, ni kuma sai na kira wani muka je wajen don ganin abinda suka binne a wurin.

“Muna ganin jini na cewa abokin nawa mu bar wajen, sai muka kira ‘yan sanda, suka zo suka kama matan.

“Duka na san su sosai, Hauwa da Zainab, suna zaune a nan haka ne. Babbar tana da shekaru kamar 35, inda ita kuma Hauwa take da shekaru 33,” cewar Bello.

Rahotanni sun bayyana cewa jaririn ya mutu, sannan an dauke shi zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunan shi ba domin gabatar da bincike.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here