Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Miji ya kashe matarsa kan taki dafa masa abincin Sahur

0
234
  • A yayin da kowa yake kokarin ganin ya samu dacewa a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
  • Sai gashi wani mutumi ya kashe matarsa da suka yi aure shekaru biyu da suka wuce akan taki dafa masa abincin sahur
  • Mutumin dai yayi amfani da bindiga ya harbe ta ne har lahira kamar dai yadda mahaifin yarinyar ya yiwa ‘yan sanda bayani

Watan Ramadana wata ne da ake so kowa ya roki gafarar ubangiji, amma duk da haka muna abubuwa kamar dabobbi, wannan wani labari ne dai zai sanya mutane su dinga mamakin halayyar dan adam.

Wani mutumi a Khyber Pakhtunkhwa ya kashe matarsa saboda kawai taki tashi ta dafa masa abincin sahur. Lamarin ya faru a yankin Kohistan, a lokacin da ma’auratan suke shirin daukar azumi.

Matar na da shekaru 19 kacal a duniya, tayi aure shekaru biyu da suka wuce. Bayan gabatar da bincike an gano cewa mijin ya kashe matar ne saboda taki dafa masa abinci.

Daga baya ‘yan sanda sun kama mutumin. A cewar uban yarinyar mijin dan gidan dan uwanshi ne, ma’ana dai kamar da ne a wajenshi.

“Mahaifin yarinyar yana yin alwala yana shirin yin sallar Asuba, kawai sai jin harbin bindiga yayi daga dakin ma’auratan,” cewar jami’in dan sanda.

“Da yaje domin ya duba abinda ke faruwa, sai ya tarar da ‘yarshi kwance cikin jini, inda tuni har mijin ya gudu,” dan sandan ya kara da cewa.

Abinda ya faru ya riga ya faru dai, ba wai kuma iya kashe ta da yayi bane, shima zai zo ya kari rayuwarshi a gidan yari.

A matsayinmu na Musulmai dole ne muyi koyi da sunnar manzon mu Annabi Muhammadu (SAW), shine abin koyi ga kowanne Musulmi na duniya. Idan har zamu dinga karanta tarihin yadda Annabi yayi rayuwarsa da matansa duk irin haka baza ta faru ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here