Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: An tsinci gawar yarinya ‘yar shekara 6 da aka yiwa fyade a Masallaci a Kaduna

0
453

An tsinci gawar wata yarinya ‘yar shekara shida da aka yiwa fyade a cikin Masallaci dake New Road, Kurmi Mashi kusa da babbar hanyar Nnamdi Azikwe, cikin jihar Kaduna.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa lamarin ya faru a ranar Juma’a, inda ya jawo hankalin mutane da yawa ciki hadda mambobin kungiyoyi zuwa wajen da lamarin ya faru.

Sai da aka sha fama da iyayen yarinyar kafin su bari a kai gawar yarinyar zuwa asibiti domin gabatar da bincik.

Da aka tuntube shi a waya, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar ASP Muhammed Jalinge ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Duk da dai babu wanda aka kama har yanzu dake da hannu da wannan laifi, amma ‘yan sandan dake aiki a yankin na Kurmin Mashi tuni sun fara gabatar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

“Kwarai kuwa, an kawo karar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Kurmin Mashi. Mutanen mu dake ofishin sun samu kiran waya akan cewa sun ga gawa kwance a cikin Masallaci.

“Sakamakon dokar hana zirga-zirga da aka sanya a jihar, ba a bude Masallacin sai ranar Juma’a kawai, sun iske gawar yarinyar da misalin karfe 3:20 na yamma gabanin sallar La’asar.

“Tuni an fara gabatar da bincike akan lamarin. Babu wanda aka kama dai har yanzu. Amma jami’an ‘yan sanda na ofishin Kurmin Mashi sun dauki lamarin da matukar muhimmanci. Saboda haka da mun kama wani zan sanar da ku.” Cewar Jalinge.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here