Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: An kama miji yana zina da karuwa a lokacin da ake jana’izar matarshi

0
538

Wani mutumi ya sanya mutane garinsu cikin rudani da mamaki, bayan an kama shi yana lalata da karuwa a lokacin da ake jana’izar matarshi.

Mutumin mai suna Luscious Chiturumani yana zaune a garin Gweru dake kasar Zimbabwe, tare da matarshi mai suna Sibongile Mthetwa, wacce ta mutu bayan ta sha fama da rashin lafiya.

A wajen taron jana’izar ta mijin yaje wajen tare da wata budurwa wacce ya bayyana musu cewar kanwarshi ce, inda ake ta girmama shi a gidansu matarshin a matsayin suruki.

Daga baya aka basu daki shi da kanwarshi don su huta , inda aka bayyana musu wasu mutanen za su zo dakin su kwana tare dasu idan dare yayi, amma sai suka ga babu wanda ya zo dakin har safiya tayi, inda su kuma suka yi amfani da wannan damar suka fara lalata da safiyar Allah.

An bayyana cewa da safe da misalin karfe 6 wani ya fito yana busa taba sigari sai ya jingina da jikin tagar dakin da suke, sai yaji ana nishi a cikin dakin ya leka yaga abinda ke faruwa.

Mutumin bai yi wata-wata ba yaje ya kira sauran mutane domin su ga abinda ke faruwa, cikin rashin sa’a basu kulle dakin ba ai kuwa mutanen suka shiga suka iske su suna lalata.

Wata ‘yar uwa ga marigayiyar mai suna Grace Mtethwa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace mijin ya jawo musu abin kunya, domin kuwa mutane sun dinga magana akan wannan abu kenan har abada.

‘Abin kunya ne ace kawuna yayi irin wannan abu,” cewar wata mai suna Humbwa Chaiwo.

“Tabbas wannan al’adace ta karnuka da rashin tunani. Daga yaya mutum zai taso tun daga Gweru yazo yayi zina a nan? Ban taba ganin abu irin wannan ba a rayuwata.

“Har yana da karfin halin da zai kawo karuwa yace wai kanwarsa ce.”

Bayan fito da su daga dakin anyi ta marin mijin marigayiyar akan abinda yayi, inda aka sanya shi a wata mota aka fita dashi daga gidan.

Tun lokacin dai wayarshi a kashe ba a kara samun shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here