Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Allah ya yiwa Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim rasuwa, kasa da awanni 24 da rasuwar Sarkin Rano

0
143

Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim ya koma ga Allah, da yake bayar da rahoton rasuwar tasa ga Daily Trust, Tijjani Sarki, daya daga cikin makusanta da masarautar Kano, ya ce za’a sallaci marigayin a yau din nan da misalin karfe 11 na rana.

Ya ce: “Na samu labarin rasuwar Jarman Kano daga bakin Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim, wanda yace Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai halarci taron jana’izar shi, wanda za ayi a kofar Kudu, da misalin karfe 11 na rana.

Marigayi Jarman Kano yana daya daga cikin manya a masarautar Kano, yayi aikin koyarwa a jami’ar Bayero dake Kano.

Marigayi mai martaba Alhaji Ado Bayero shine ya bashi mukamin Jarman Kano, bayan mutuwar tsohon Jarman Kano na wancan lokacin, ALhaji Adamu Dankabo, shugaban kamfanin jirgin sama na Kabo Air.

Wannan dai na zuwa ne cikin kasa da awanni 24 da rasuwar Sarkin Rano, wanda ya rasu a jiya.

Allah Ubangiji ya jikansu da gafara Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here