Inda ranka kasha kallo: Sabuwar kwalliyar rina gemu kalar kayan sawa ta dauki hankulan jama’a a yanar gizo

0
971

Duniya labari kamar yadda Hausawa kance inda ranka kasha kallo wannan magana haka take domin kuwa idan har da ran naka zaka yi ta ganin sababbin abubuwa na ban mamaki da al’ajabi.

Wani matashi ne ya bullo da wani sabon salon kwalliya wadda duk kalar kayan da ya saka haka zai rina kalar gemunsa, wannan kwalliya tasa ta kasance sabon abu da ya dauki hankulan jama’a a yanar gizo.

Kamar dai yadda kowa ya sani a Musulunce da al’ada ta Hausawa mutane kan iya rina gemu da shuni ko ayi masa lalle, inda shi kuma wannan saurayi ya zamanantar da wannan al’ada wacce ta saka kowa yake tofa albarkacin bakinsa, wasu kuwa sun mayar da lamarin abin wasa dake tsakanin Kanawa da Zazzagawa, inda mutanen Kano ke cewa ‘yan Kaduna ne da wannan sabon salo, su kuma ‘yan Kaduna suke cewa wannan matashi dan jihar Kano ne.

Sai dai har ya zuwa yanzu ba a san ainahin suna ko kuma daga inda wannan matashin saurayi yake ba.

To ‘yammata masu kaunar samari masu aje gemu ga fa dama ta samu shin mai zaku ce game da wannan dan gayun saurayi da ya fito da sabon salo na gemu.

Ga dai hotunan saurayin da irin shigar da yake yi:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here