Ina so na zama fitaccen mawaki idan na mutu na shiga Aljannah – Obasanjo

0
862

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce yana so ya shiga Aljannah ko dan ya shiga cikin kungiyar mawakan Aljannah.

Obasanjo ya bayyana haka a lokacin da yaji wata waka da aka yi a cocin Apostolic Faith Church dake Igbesa, jihar Ogun. Obasanjo ya yiwa Kiristoci gargadi a Najeriya da su shirya zuwan Isa Al-Masihu a karshen duniya.

“Ya kamata ku shirya sosai domin ubangiji yana nan dawowa. Ina da aboki da yace idan muka mutu muka shiga Aljannah sai mun gaji da yiwa ubangiji waka, kuma Aljannah za ta zama kamar gidan yari babu dadin zama.

“Amma ni abinda na gani a mahangata shine, zan shiga Aljannah, zan kuma shiga cikin kungiyar mawaka. Idan har wannan shine misalin yadda ake yabon ubangiji a Aljannah, to zan so shiga wannan kungiya. Idan har abinda na gani a nan shine misali na yadda Aljannah take to zan so shiga Aljannah.

“Isah Al-Masihu ya zo duniya ne domin ya nuna mana hanyar rayuwa ya kuma ceto mu daga halaka.

“Allah zai iya gyara Najeriya, amma dole sai mun kira shi ya shigo cikin rayuwar mu tukunna. Abinda zamu yi a kasar nan na hannun mu.” Ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here