Ina matukar farin ciki akan rikicin dake faruwa a APC, ina fatan za su cigaba da samun matsala – Nyesom Wike

0
306

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce yana cikin matukar farin ciki akan rikicin dake faruwar a babbar jam’iyya mai mulki ta APC, sannan yana addu’ar jam’iyyar ta cigaba da samun matsala da samun rikici.

Wike wanda yake jigo a babbar jam’iyya ta PDP, ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise TV.

“Ina cikin farin ciki da irin rikicin dake faruwa a APC. Ba hurumi na bane na taimakawa APC ta samu hadin kai. Idan baku manta ba muma mun samu namu rikicin a lokacin Ali Modu Sheriff, kuma APC tayi murna akan haka.

“Addu’a ta ita ce ina fatan su cigaba da samun wannan matsala a tsakaninsu. Mun riga mun kara kwatar wata jihar. Abin takaicin, APC ba wai jam’iyyar siyasa ba ce. Dama sun hadu ne kawai domin su kwaci mulki.

“Ina son jam’iyya ta ta zama akan mulki, ba zan iya yi musu addu’a akan kada su samu matsala ba. Ina fatan za su cigaba da samun rikici a tsakaninsu kullum sannan kuma jam’iyyata ta cigaba da daukaka,” ya ce.

Dangane da lashe zaben dan takarar gwamnan Edo a jam’iyyar PDP da Godwin Obaseki yayi kuwa, Wike ya ce bashi da wata matsala da hakan.

Ya ce shi babbar damuwar shi shine kowanne dan jam’iyya na jihar ya tashi tsaye yayin da jihar ke shirin gabatar da zaben gwamna a ranar 19 ga watan Satumbar wannan shekarar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here