Ikon Allah: Miji ya rasa inda zai saka kansa bayan ya gano tagwayen da matarsa ta haifa masa daya ba nashi bane

1
431

Wani magidanci ya rasa bakin magana, bayan ya gano cewa jariran tagwaye da aka haifa masa daya daga ciki ba nashi bane.

Magidancin ya gano hakan ne bayan ya kai jariran gwajin DNA, a matsayin hanya guda daya da za ayi musu rijistar haihuwa a kasar China, kamar yadda ma’aikacin lafiya ya sanar da manema labarai.

Mutumin dan kasar China, wanda ba a bayyana ko waye ba, yayi mamaki matuka da wannan sakamakon gwaji da aka yi, inda hakan ke nuni da cewa matarshi na kwanciya da wani a titi.

Deng Yajun, wacce ta gabatar da binciken, ta ce ba kasafai ake samun irin wannan lamari ba, inda ta ce a cikin mutum miliyan 10 dakyar ake samun daya da irin wannan.

“Na farko sai mace ta samar da kwayayen haihuwa guda biyu a cikin wata daya domin ta samu tagwaye,” cewar Ms Deng, wacce take darakta ta cibiyar gano bayani ta birnin Beijing Zhongzheng dake kasar China.

Na biyu dole sai ta sadu da maza guda biyu a tsakanin lokaci kankani idan har hakan za ta faru.”

“Sakamakon ya nuna cewa yaran suna da uwa daya, amma ubansu ba daya bane. Suna da akalla iyaye maza guda biyu,” cewar Ms Deng.

Abu makamancin haka dai ya taba faruwa a kasar ta China a shekarar da ta gabata. Inda wata mata ta bayyana cewa ta ci amanar mijinta a wani lokaci bayan gwajin DNA da aka yiwa tagwayen ya nuna gaskiyar cewa daya daga ciki ba ‘ya’yanshi bane.

Dama kuma mijin yana ta mamaki yadda aka yi daya daga cikin ‘ya’yan baya kama da shi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here