Ikon Allah: Mata ta haihu bayan shafe shekara 10 dauke da ciki

0
455

Wata mata mai suna Elizabeth Packal, mai shekaru 23, ‘yar asalin kasar Togo dake zaune a jihar Oyo, an ruwaito cewa ta haifi jaririya bayan shafe shekara 10 da ciki.

Wakilin Legot.ng na jihar Oyo, Imran Khalid, ya ruwaito cewa bayan ta haihu, Elizabeth ta bayyana cewa bata san wanda yayi mata cikin ba.

Elizabeth wacce ke zaune a kauyen Eiyeosoka, dake karamar hukumar Atisbo cikin jihar Oyo, ta haihu a ranar 20 ga watan Maris, 2020 da misalin karfe 7:45 na dare a Alaafia Tayo Clinic, wanda yake a Irawo-Owode, cikin karamar hukumar ta Atisbo.

Bayan gabatar da wani bincike, likitan asibitin Dr Okawoyin David, ya bayyana cewa a lokacin da suka kawo Elizabeth asibitin, ya tambaya inda aka yi mata gwajin ciki, mahaifinta Ahmadu Guruma Packal ya bayyana cewa basu da masaniya game da ciwonta, inda ya kara da cewa sun kai ta asibitoci da dama amma an kasa gano abinda ke damunta.

Guruma ya kara da cewa daga bayane wasu abokananshi suka bashi shawara akan ya kai ta wannan asibitin, inda kuma ta haifi ‘ya mace.

Da Guruma da shi likitan sun ce duka sun yi mamaki da suka ga Elizabeth ta haihu.

Dr Olawoyin ya ce a lokacin da suka kawo ta ya tambaya tun yaushe ne bata da lafiya, sai ta amsa mishi da cewa tun shekarar 2010.

Likitan ya ce ya bukaci da su kai ta wani babban asibiti a Ago-Are ko kuma Saki, amma mahaifinta yaki amincewa, har sai da budurwar ta haihu.

Likitan ya ce akwai yiwuwar ciwon ya jima yana cin jikinta tun kafin ta dauki cikin, saboda bayan ta haihu cikin nata dai yana kumbure bai sace ba, kamar dai akwai wani cikin a tare da ita.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san wanda ya yi mata cikin ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here