Idan kuka daina yawo tsirara maza za su daina yi muku fyade – Cewar ‘yan majalisa 2

0
1771

‘Yan majalisar wakilai na tarayya guda 2 sun bayyana cewa yawan fyade zai ragu a Najeriya idan mata suka fara sanya kaya da basa nuna tsiraici.

A ‘yan kwanakin nan dai mutane na ta magana akan fyade a Najeriya, bayan fyade da aka gabatar wadanda suka dau hankali har sau uku, inda har biyu daga cikin matan suka rasa rayukansu sakamakon haka.

Uwaila Omozuwa, budurwa mai shekaru 22 dake jami’ar Benin, anyi mata fyade a makon da ya gabata, inda kuma aka kasheta a cikin coci, haka kwanaki kadan bayan nata lamarin ita ma wata budurwa mai shekaru 18 da suna Barakat Bello, an yi mata fyade kuma aka kashe ta a cikin gidansu a ranar Litinin 1 ga watan Yuni.

Uwaila Umozuwa wacce aka yiwa fyade aka kasheta a cikin coci Photo Source: Punch

Haka rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ita ma ta bayyana kama wasu mutane 11 da suka yiwa wata yarinya mai shekaru 12 fyade a wurare daban-daban.

A wani zama da suka yi a dakin majalisar wakilai a ranar Alhamis 4 ga watan Yuni, Rotimi Agunsoye, dan majalisa mai wakiltar Kosofe dake jihar Legas, ya taso da maganar muhimmancin daukar mataki akan yawan samun fyade da ake yi a Najeriya.

Barakat Bello budurwa ‘yar shekara 18 da aka yiwa fyade aka kashe

A yayin tofa albarkacin bakinsu, ‘yan majalisu da yawa sun bayyana ra’ayoyinsu, inda wasu suka bayyana a yankewa masu laifin hukuncin kisa don kawo karshen irin wannan ta’asa a kasar.

Da yake bada tashi gudummawar, Henry Okon Archibong, dan majalisa mai wakiltar Itu/Ibiono Ibom dake jihar Akwa Ibom, ya ce yana goyon bayan duk wani hukunci da za a yankewa masu fyade, amma kuma yana ganin cewa hukuncin ka dai ba zai isa ba ya kawo karshen matsalar ba.

Dan majalisar mai shekaru 53 ya ce, idan aka yi duba babban abinda yake jawo fyade ya samo asali akan yanayin dabi’ar da muke da ita a Najeriya.

“Iyaye sun gaza, Malaman addini sun gaza, makarantu ma sun gaza tun daga makarantun firamare.

“Yanzu mun san cewa saboda matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, iyaye basa samun damar zama da ‘ya’yansu, kuma a wannan lokacin ne ya kamata a koyawa yara darasi.

“Idan har muka samu matsala bamu koya musu a wannan lokacin ba, babu wata hanya da zamu koyar da su,” ya ce.

Henry Okon mata za su taimaka wajen rage fyade idan suka daina nuna tsiraici Photo Source: Facebook/Itu/Ibiono Ibom 2019

Archibong ya ce mata suna taimakawa matuka wajen yi musu fyade sakamakon irin shigar da suke yi.

Haka shima a nashi jawabin Ahmed Jaha Babawo, dan majalisar wakilai mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok dake jihar Borno, ya bayyana abubuwa guda biyu inda ya bukaci ‘yan majalisar su zaba.

Na farko Babawo ya bukaci cewa duka gwamnatocin jihohi su sanya dokar bawa yara ‘yanci, da kuma dokar yaki da fyade.

Haka kuma ya bukaci a yanke hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai ga wanda aka kama da laifin fyade.

Abu na biyu da ya bukata shine dole matan Najeriya su dinga yin shiga ta kamala wacce baza ta dauko hankalin maza kansu ba.

“Mata su koyi yadda ake sanya kaya na kamala domin gujewa irin wannan cin zarafi daga wajen maza, saboda maza ba itatuwa bane,” ya ce.

Ahmed Jaha Babwo Photo Source: Ahmed Jaha Babawo Facebook Page

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here