Idan kaga mutum ya tsaneka haka kurum ba tare da kayi masa laifi ba to hassada ce da bakin hali – Zahra Buhari

1
336

‘Yar gidan shugaban kasa Zahra Buhari, ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram, inda ta yi magana akan yadda mutane suke tsanar junansu babu gaira babu dalili.

Zahra ta ce tsanar mutum ba tare da yayi maka wani laifi ba, alama ce ta hassada da kishi a tattare da mutum.

Diyar shugaban kasar ta shawarci duka masu irin wannan al’ada da suyi maza su nemi mafita akai. Ta bayyana cewa ita ma ta sha fama da irin wannan abu, inda ta kuma yi bayanin yadda ta samu ta nemawa kanta mafita.

“Maganar da zanyi yau ba sabon abu bace, zanyi magana ne akan muhimmin abu. Na sha jin mutane na shiga wani hali, ana sanya musu karan tsana, cin mutunci, da wariya, ba tare da sunyi wani laifi ba, na jima ina nazari akan wannan abu. Na gano cewa dalili guda daya ne shine Hassada.

“Kunga idan mutum bai yi maka komai ba, kuma kaga baka da aiki sai kalubalantar shi da ci masa mutunci, ina ganin ya kamata mutum ya binciki kanshi ya gano inda matsalar take.

“Idan dama kai da wannan mutumin baku yin shiri, babu matsala, kayi masa sallama, ba dole ne sai kunyi fada ko cacar baki ba.

“Sannan kuma idan kai ne wanda aka tsana ake ciwa mutunci, na tabbata babu dadi saboda nima an sha yi mini, inda mutane suka sako ni a gaba suna ta yi mini abinda suka ga dama.

“Ba damuwa zaku iya yi mini duk abinda kuka ga dama, amma fa ku sani kowa fa akwai ranar sa, saboda idan kun ci mini mutunci hakan ba yana nufin kuna da ikon tunzura ni ba.

“Tabbas idan ana yi maka irin haka dole ka shiga damuwa, kafin ka zo ka saba. Amma ina da hanyar da nake ganin zaku iya bi domin shawo kan irin wannan lamarin.”

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here