Hukuncin kisa yayi kadan akan masu laifin fyade – Ministar Abuja, Dr Ramatu Aliyu

0
919

Karamar ministar Abuja, Dr Ramatu Aliyu, tayi kira da a dauki kwakkwaran mataki akan masu yiwa mata fyade babu gyara babu dalili.

A wata sanarwa da mai taimaka mata na musamman a fannin sadarwa, Mr Austine Elemue, ya fitar, ministar ta bukaci a dinga dandake masu fyaden. A cewar ta hakan zai zama babban darasi ga wasu.

Ramatu ta bayyana cewa ma’aikatar ta na aiki da duka hukumomin tsaro da sauran hukumomi domin haramta safarar mutane sannan kuma a tabbatar da hukunci ga wadanda aka kama suna yi.

Aliyu, wacce ta bayyana yiwa yara fyade a matsayin babban ta’addanci, ta ce hukuncin kisa yayi kadan ga masu wannan laifi.

Ta ce idan har aka yanke musu hukuncin kisa, da sun mutu shikenan baza su tuna da komai ba da suka yi.

‘Za mu sanya kowa da kowa a wannan yaki da muke akan fyade. mun fara bincike akan wani da yayi laifin, kuma zamu gano shi.

“Tare da hadin guiwar duka hukumomin tsaro da NAPTIP, muna nan muna sanya ido, duk wanda muka kama da wannan laifi sai mun tabbatar matacce ya fishi jin dadi.

“Hukuncin kisa yayi kadan ga wadannan mutanen, hukunci irinsu dandaka zai yi aiki, saboda da mun kashe su shikenan babu wani abu da za a gani ko za su gani su tuna.

“Saboda haka ayi musu dandaka, a sake su sai kuma muga yadda za su yi,” cewar ta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here