A jiya Asabar ne 27 ga watan Yuni, hotunan wata yarinya da bata fi shekara goma sha biyu ba da wani matashi da akalla zai kai shekaru ashirin da bakwai zuwa talatin suka fara karade kafafen sadarwa na zamani, inda aka nuno so sun dauki hotunan kafin aure da ake kira da Pre-Wedding Pictures, alamu dai sun nuna cewa suna dab da yin aure, hakan kuwa ya jawo kace-nace da sabanin ra’ayoyi daban-daban.

Sai dai mutane da yawa suna yaba wannan dabara ta iyayen da suke aurar da ‘yarsu tun tana karama, musamman ma idan aka yi duba da yadda zamani gurbace.
Wasu kuwa na ganin cewa kamar an shiga hakkin yarinyar ne, inda suka bayyana cewa wannan aure bai kamata ayi ba kwata-kwata.

Ga dai wasu daga cikin ra’ayoyin mutanen da muka samu damar tattaro muku, inda wata mai suna Salma Edrees Maimurjani ta ce, da zinar wuri gwara auren wuri, ga dai cikakken rubutun da tayi a shafinta na Facebook:
Ita kuwa wata mai suna Khadija S Umar cewa tayi, ya kamata a fito a yi magana akan fyaden da ake yiwa yara kanana, inda ta ce:
Duk da dai ba a samu wanda ya wallafa rubutu na musamman don sukar auren ba, amma ga kadan daga cikin wadanda suka soki auren a sashen tsokaci.


Shin kuna ganin wannan aure ya dace, ko kuwa zulunci ne kamar yadda wasu ke fada.
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com
Aurensu ba haramun bane Amma ana barin halal Dan kunya ilimi shine abu mafi mashimmanci agurin wannan yarinyar
Comment:allah yasama auren albarka yatsaresu daga sharrin shaidan amin
Da so samu ne, ango ya Kai amariyar sa makaranta bayan aure. Kana ya haqura har sai ta qara girma, Amma batun laifi a ajiyeshi a gefe.