Hotuna: Yaron dan shekara 10 ya yiwa yarinya ‘yar shekara 13 ciki

0
5577

Yarinya ‘yar kasar Rasha da ta bayyana cewa wani yaro dan shekara goma ne mahaifin yaron dake cikinta, an garzaya da ita asibiti yayin da haihuwa ta zo mata da matsala.

Yarinyar mai suna Darya Sudnishnikova tana da shekara 13 ta bayyana a talabijin inda ta bayyana cewa yaro dan shekara 10 mai suna Ivan, wanda aka fi sani da Vanya, shine yayi mata ciki.

A watan Janairu ne dai Darya ta bayyana cewa: “Vanya ne ya bukaci muyi lalata, ni kuma ban damu ba. Sai ya rufe kofar dakin da muke ciki ya bar mukullin a jiki saboda kada mahaifiyarsa ta bude.”

Ivan wanda yanzu yake da shekaru 11 a duniya yayi alkawarin rainon jaririn tare da mahaifiyarsa.

Yanzu dai akwai alamu dake nuna cewa za a iya haifar yaron bakwaini, wato kafin lokacin kammala halittarsa.

Wani bidiyo dake yawo ya nuna Darya kwance a asibiti an sanya mata na’ura dake gwada bugun zuciyar jaririn.

Darya wacce ke da shekaru 14, wacce ta zama fitacciya a shafukan sadarwa na kasarsu, idan mutane kusan rabin miliyan ke bin shafinta, ta cewa mabiyanta: “Maganar gaskiya ina tsoron haihuwa, shin wane irin ciwo ake ji idan an zo haihuwa?

Daga baya kuma ta ce akwai yiwuwar za ayi mata tiyata ne a ciro dan. ta kara wallafa cewa: “An bayyana mini cewa ba zan iya jurewa zuwa watan Agusta ba, amma zanyi kokari naga jaririna ya zo cikin koshin lafiya.”

“Yanzu na fi tsoro fiye da da, hatta sauka daga kan gadona tsoro nake ji, saboda ina tsoron komai zai iya faruwa.

“An hana ni fita, abinci ma kawo mini ake yi.

Yarinyar wacce ke a karatu a makarantar sakandare ta bayyana cewa ciki yana da matsalolinshi da suka hada da laulayi, ciwon zuciya, da dai sauransu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here