Hotuna: ‘Yar gidan Donald Trump ta gama shiri tsaf za ta auri dan Najeriya

1
6227

Tiffany Trump, diya a wajen shugaban kasar Amurka Donald Trump, an tabbatar da tana soyayya da wani matashin saurayi dan asalin jihar Legas mai suna Micheal Boulos.

Micheal dan gidan wani hamshakin mai kudi ne a Najeriya, masoyan sun shafe shekara biyu kenan yanzu suna soyayya.

Soyayyar Tiffany da Micheal dai na cigaba da karfi, inda ake ganin a kowanne lokaci suna iya yin aure.

Masoyan sun hadu a wajen hutun da suka halarta a Greece a watan Yulin shekarar 2018.

Har yanzu dai ba san ko shugaba Donald Trump ya amince diyar tashi ta cigaba da soyayya da dan Najeriyan ba.

Idan ba a manta ba Trump ya sha cin mutunci da zagin Najeriya a lokuta da dama. A wani rahoto da PageSix ta ruwaito, masoyan sun yi wata ganawa ta musamman, inda har shi saurayin ya hadu da dangin Tiffany baki daya.

Micheal Boulos shine ke da gadon kamfanin SCOA dake Najeriya, kamfanin ya samo asali a jihar Legas, inda suka yi suna wajen sayarda da kayan kwalliya na gwal da zinare.

A shekarar 1950, danginsu Micheal sun sake fadada kasuwancinsu, inda suka fara shigo da babura na Miele, Durkopp da Goricke a shekarar 1959, sannan kuma suka koma shigo da babur kirar Suzuki.

Tsakanin shekarar 2010 da shekarar 2016, kamfanin ya wakilci kamfanin Piaggio dake Indiya, inda yake hada keke napep a Najeriya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here