Hotuna: Yadda saurayi yaje kan kabarin mahaifiyarsa don ya nuna mata takardun kammala karatunsa

0
570

Ka dauka mahaifiyarka ce ta dinga fadi tashi tana kashe maka duka kudin da take samu wajen ganin ka samu ilimi mai kyau rayuwarka tayi kyau a karshe, amma a lokacin da ya kamata ta fara jin dadin wahalar da tayi maka sai Allah ya dauki rayuwarta.

Irin wannan hali ne wani dalibin kwaleji na jihar Kano, mai suna Isah Salisu Alhassan ya shiga, wanda ya kammala bautar kasa, ya dauki takardunsa yaje har kan kabarin mahaifiyarsa don ya nuna mata.

Saurayin ya wallafa hotunan masu ban tausayi a lokacin da ya durkusa a gaban kabarinta yake nuna mata takardun na shi na kammala karatu.

Dalibi ya kai takardunsa ga mahaifiyarsa da ta rasu makabarta Photo Source: Pulse.ng

A cewar Isah, mahaifiyarshi ta rasu a watan Janairun wannan shekarar, inda ya rage bai fi saura watanni biyar ya kammala bautar kasa ba, a lokacin da sauran ‘yan uwansa masu bautar kasa ke daukar takardunsu zuwa gidajensu ga ‘yan uwansu da abokanan arziki, shi sai ya wuce kai tsaye zuwa ga kabarin mahaifiyarsa don nuna godiya akan wahalar da tayi a kanshi.

Dalibi ya kai takardunsa ga mahaifiyarsa da ta rasu makabarta Photo Source: Pulse.ng

“A shekarar 2008 lokacin da take korani makaranta da bulala, takan ce kaje makaranta kayi karatu ko ka samu ka zama wani a rayuwa.

“Yanzu iya kashinta ne kawai ya rage a cikin kabari, kuma ta rasu a watan Janairun shekarar 2020, watanni biyar na kamalla bautar kasa ta.

“Yayin da kowa yake kai takardunsa ga ‘yan uwansa da abokanan arziki, sai ni kuma na taho makabarta kai tsaye don na nunawa mahaifiyata nawa.

‘Allah ka jikan iyayen mu.”

Dalibi ya kai takardunsa ga mahaifiyarsa da ta rasu makabarta Photo Source: Pulse.ng

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here