Hotuna: Yadda mage ta kai diyarta asibiti bayan ta kamu da rashin lafiya

0
627

Wani hoton mage da aka dauka a wani asibiti da ba a bayyana sunanshi ba a birnin Istanbul na kasar Turkey, ya yadu a shafukan sadarwa. A rahoton Bored Panda, wani mutumi mai suna Merve Ozcan shine ya dauki hoton.

Hoton ya nuna lokacin da wata mage ta kai diyarta asibitin mutane a yayin da ‘yartan ta kamu da rashin lafiya. Ta dauki diyartan da bakinta ta taka a hankali har zuwa asibitin.

Kafafen sadarwa dai sun ruwaito cewa mutanen kasar ta Turkey suna girmama dabbobi sosai da basu kulawa.

A cikin hoton dai za a ga yadda likitoci suka taimakawa magen a lokacin da ta isa asibitin.

“Yau muna cikin asibiti kawai sai muka ga mage ta shigo da diyarta a baki,” cewar Merve Ozcan, wanda ya wallafa hoton a shafinsa na Twitter.

A cewar Bored Panda, wasu jaridu na kasar ta Turkey sun ruwaito cewa a yayin da likitocin suke duba diyar magen, an baiwa uwar madara sannan aka bata wuri ta jira.

Daga baya an ruwaito cewa magen ta samu lafiya bayan likitocin sun duba ta.

Ga dai hotunan su a kasa:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here