Hotuna: Tsohuwa ta fashe da kuka bayan dan bautar kasa ya gina mata gida sabo dal

0
357

Wani dan bautar kasa mai suna Nyah Patrick, ya bayar da gida mai dakuna guda biyu ga wata tsohuwa mai suna Mrs Blessing Onyekwere a kauyen Inyia dake Ikwuano jihar Abia.

Da yake bayani a lokacin da yake kaddamar da gidan gareta, dan bautar kasar, ya ce ya yanke shawarar gina mata gidan ne bayan ya hadu da ita shekarar da ta wuce ita da ‘ya’yanta, a lokacin da ake ci musu mutunci ake neman korarsu daga gidan da suke yin haya.

Nyah ya ce a lokacin da ya isa wajen bautar kasar shi, babban abinda ya sanya a ranshi shine ya siyo litattafai na rubutu guda 2,000 ya rabawa dalibai na makarantar sakandare ta Ibere, amma daga baya ya canja shawara a lokacin da ya hadu da wannan matar.

Photo Source: Correct NG

Ya ce daga baya ya shiga cikin garin domin ya nemi wadanda za su dauki nauyin aikin.

KU KARANTA: Jerin manyan kabilu guda 10 a nahiyar Afrika da suka fi yawan al’umma

Da take nuna godiyarta, Mrs Blessing Onyekwere, wacce tsananin jin dadi ya sanya ta fashe da kuka, ta yiwa dan bautar kasar godiya, inda tayi masa addu’ar Allah yayi masa albarka da wannan abun alkhairi da yayi mata ita da ‘ya’yanta.

Photo Source: Correct NG

Da take kaddamar da gidan ga matar, shugabar hukumar NYSC ta jihar ta Abia, Lady Bona Fasakin ta bayyana wannan dan bautar kasa a matsayin dan kasa na gari. A karshe ita ma ta sanya masa albarka.

A nashi jawabin, shugaban karamar hukumar Ikwuano, Honourable Stanley Ejigbo, shima ya yabawa wannan dan bautar kasa akan wannan namijin kokari da yayi, inda ya ce duk abinda mutum ya shuka shi zai girba, idan khairan khairan, haka ma idan sharri ne sharri zai girba.

Photo Source: Correct NG

Haka yayi alkawarin gyara gidan yadda ya kamata koda matar da ‘ya’yanta za su samu damar shiga gidan da wuri.

Kaddamar da gidan dai ya samu halartar mutane da yawa daga kauyuka daban-daban na wannan yanki, ciki kuwa hadda ‘yan uwa da abokanan arzikin wannan dan bautar kasa, shugaban makarantar da yake aiki a ciki da kuma shugabannin hukumar NYSC na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here